Al’ummar Duniya na ci gaba da nuna alhini baya ga aikewa da sakon ta’aziyya game da mutuwar zakaran kwallo na Duniya Pele, wanda ya koma ga mahaliccinsa a jiya alhamis yana da shekaru 82 bayan fama da doguwar jinyar cutuka daban-daban ciki har da ciwon koda da kuma kansar hanji.
Dubban mutane ne suka kewaye asibitin da Pele ya mutu na Albert Einstein dauke da hoton zakaran kwallon daga daren jiya zuwa wayewar yau juma'a yayinda tuni wasu suka fara ajje furanni baya ga rere waken bankwana ga zakaran da ake gani a matsayin gangaran da babu kamarsa a fagen tamaula.
Filin wasa na Maracana da ke birnin Rio de Jeneiro a Brazil, kwana ya yi kunne da wata wutar ban girma da ke walwali dauke da hoton tauraro Pele yayinda filin wasa na Wembley a London ya yi makamancin ban girman baya ga bayyana Pele a matsayin abin koyi ga dubunnan 'yan wasa.

Comments
Post a Comment