An rantsar da Luiz Inacio Lula da Silva a matsayin shugaban kasar Brazil a wa’adi na uku a wannan Lahadin, inda ya yi wa kujerar shugabancin kasar kome bayan ya doke Jair Bolsonaro mai ra’ayin rikau a zaben watan Oktoban da ya gabata.
Lula da ya taba jagorantar kasar a baya, ya sake darewa kan karagar mulki ne bayan ya sha rantsuwa a zauren majalisar dokokin kasar, inda ya lashi takobbin kare da kuma biyayya ga dokokin kasar mafi girmar tattalin arziki a yankin Latin Amurka.
Gabanin shan rantsuwar, sai da aka yi shiru na tsawon minti guda domin karrama tsohon fitaccen dan kwallon kafar kasar, wato Pele da kuma tsohon shugaban Darikar Katolika ta Duniya Fafaroma Benedict da suka mutu a ‘yan kwanakin nan.
Ya kuma yi alkawarin sake gina kasar tare da al'ummarta.
Komawar Lula fadar shugabancin Brazail na nuni da wani gagarumin al’amari, ganin cewa, kasa da shekaru biyar kenan da aka kama shi tare da garkame shi a gidan yari kan wasu zarge-zargen cin hanci da rashawa masu sarkakiya.

Comments
Post a Comment